Colossians 4

1Masu bayi, ku riƙe bayinku da kyau da kuma daidai, domin kun san cewa ku ma kuna da Ubangiji a sama.

Ƙarin Umarnai

2Ku nace da yin adduʼa, kuna zaman tsaro da kuma godiya. 3Ku kuma yi mana adduʼa, mu ma, don Allah yǎ buɗe ƙofa saboda saƙonmu, don mu iya yin shelar asirin Kiristi, wanda saboda shi nake cikin sarƙoƙi. 4Ku yi adduʼa yadda zan yi shelarsa, yadda ya kamata. 5Ku zama masu hikima a yadda kuke maʼamala da waɗanda suke ba masu bi ba; ku kuma yi amfani da kowane zarafi. 6Bari maganarku kullum ta zama da ladabi da kuma daɗin ji, domin ku san amsar da ta dace ku ba wa kowa.

Gaisuwa ta Ƙarshe

7Tikikus shi ne ƙaunataccen ɗanʼuwan nan, wanda ya yi aiki da aminci a hidimar Ubangiji tare da mu, zai kuwa faɗa muku dukan labari game da ni. 8Ina aikansa domin yǎ ƙarfafa ku ta wurin faɗa muku yadda muke a nan. 9Yana zuwa tare da Onesimus, ƙaunatacce da kuma amintaccen mai bin nan, wanda yake ɗaya daga cikinku. Za su gaya muku dukan abin da yake faruwa a nan.

10Aristarkus yana a kurkuku tare ni. Yana gaishe ku, haka ma Markus, wanda kakansa ɗaya ne da Barnabas. (Shi ne na riga na yi magana a kansa, na ce muku in ya zo, ku karɓe shi hannu biyu-biyu). 11Yesu (wannan da muke kira Yustus) shi ma yana gaisuwa. Waɗannan ne kaɗai Yahudawa masu bi a cikin abokan aikina saboda mulkin Allah. Sun kuma zama da taimako a gare ni. 12Efafaras naku, mai hidimar Kiristi Yesu, yana gaisuwa. Kullum yana adduʼa dominku sosai, don ku san cikakken abin da Allah yake so ku yi don kuma ku yi shi cikakke. 13Na tabbatar muku, cewa yana aiki ƙwarai dominku da kuma domin waɗanda suke a Lawodiseya da Hiyerafolis. 14Luka ƙaunataccen likitan nan, da kuma Demas suna gaishe ku. 15Ku miƙa gaisuwata ga ʼyanʼuwan da suke a Lawodiseya, musamman ga Nimfa da kuma ikkilisiyar da take taru a gidanta.

16Bayan an karanta muku wannan wasiƙa, ku tabbata an karanta ta kuma a ikkilisiyar Lawodiseyawa; ku ma ku karanta wasiƙar da ta zo daga Lawodiseya.

17Ku faɗa wa Arkiffus yǎ tabbata ya ƙarasa aikin da ya karɓa cikin Ubangiji.

18Ni Bulus ne nake rubuta muku wannan gaisuwa da hannuna. Ku tuna da sarƙoƙina. Alherin Allah yǎ kasance tare da ku.

Copyright information for HauSRK